2020-04-15 11:07:51 cri |
Dangane da wannan batu, babban magatakardan MDD Antonio Guterres, ya bayyana a jiya cewa, dole ne a goyi bayan hukumar kiwon lafiyar WHO, wadda ke da muhimmiyar ma'ana ga kasa da kasa, wajen cimma nasarar yaki da cutar numfashi ta COVID-19.
Kafin haka kuma, kasar Amurka ta zargi hukumar WHO, ta kuma sanar da dakatar da biyan kudin kasancewar ta mamba a hukumar. Dangane da wannan batu, a ranar 8 ga watan nan, babban sakataren hukumar WHO Tedros Adhanom Ghebreyesus, ya ce, bai dace a mai da annobar cutar numfashi ta COVID-19 a matsayin sharadin siyasa ba, kuma ya kamata wurare daban daban a matakin kasa, da ma sassan kasa da kasa su yi hadin gwiwa wajen yakar annobar. (Maryam)
| ||||
® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China