2020-04-16 15:55:09 cri |
Cibiyar harkokin cinikayyar waje ta kasar Sin, wadda ke shirya bikin baje kolin kayayyakin da ake shigowa da su, da wadanda ake fitarwa daga kasar ta Sin, ko "Canton fair" a takaice, ta sanar da sunan babban kamfanin nan na fasahar sadarwar na kasar Sin wato Tencent, a matsayin wanda zai samar da hidimomin fasahar sadarwa, yayin baje kolin Canton karo na 127 dake gudana a birnin Guangzhou, wanda a wannan karo zai gudana ta yanar gizo, tsakanin tsakiyar watan Yuni zuwa karshen watan Yuli dake tafe.
Barkewar cutar numfashi ta COVID-19 ne dai ya sanya aka dage bikin na Canton fair, wanda a baya aka shirya budewa a jiya Laraba. Wannan ne kuma karon farko a tarihin baje kolin, da za a gudanar da shi ta yanar gizo. (Saminu)
| ||||
® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China