Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Sin da Afirka na tabbatar da shawarwari da juna kan halin da 'yan Afirka ke ciki a lardin Guangdong
2020-04-15 20:45:42        cri
A yau Laraba, kakakin ma'aikatar harkokin waje ta kasar Sin, Mr. Zhao Lijian ya bayyana a birnin Beijing cewa, a kwanakin nan, Sin da kasashen Afirka na tabbatar da tuntubar juna da yin shawarwari yadda ya kamata dangane da halin da 'yan Afirka mazauna lardin Guangdong na kasar ke ciki.

A yayin taron manema labarai da aka shirya a wannan rana, Mr. Zhao Lijian ya yi nuni da cewa, manufar Sin ta sada zumunta da kasashen Afirka ba ta sauya ba, kuma tana daukar matakai na bai daya kan 'yan gida da kuma baki da ke lardin Guangdong a yayin da ake fuskantar matsanancin hali na shigowar cutar COVID-19 daga ketare. Ya ce, "Da yawa daga cikin gwamnatocin kasashen Afirka da ma jakadunsu a kasar Sin suna ganin cewa, domin kare lafiyar al'ummar Sinawa da ma baki 'yan kasashe daban daban ne ake daukar matakan a lardin Guangdong, don haka ya kamata baki mazauna wurin su ba da hadin kai da goyon baya. Kasashen Afirka na jinjinawa kasar Sin kan yadda take ba da muhimmanci wajen kulawa da su, sun kuma lura da cewa, halin da baki 'yan Afirka ke ciki ya inganta sosai a sassan da abin ya shafa. Baya ga haka, wasu abokanmu na Afirka sun nuna cewa, bisa binciken da aka yi, an tabbatar da cewa, wasu hotunan bidiyon da ke yawo ta yanar gizo an yi musu kwaskwarima, ba ainihin gaskiyar lamarin da ya faru ba ne. Don haka, kamata ya yi Sin da Afirka su yi taka tsantsan a kan wadannan bayanan da ka iya sanya al'umma yi musu bahaguwar fahimta.(Lubabatu)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China