Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Kasar Sin za ta tura tawagogin masana kan annobar COVID-19 zuwa kasashen Habasha da Burkina Faso
2020-04-15 20:20:24        cri
Mai magana da yawun ma'aikatar harkokin wajen kasar Sin Zhao Lijian, ya bayyana cewa, kasarsa ta yanke shawarar tura tawagogin masana kan yaki da annobar COVID-19 zuwa kasashen Habasha da Burkina Faso, don kara karfin matakan kasashen na kandagarki da hana yaduwar annobar .

Zhao ya bayyana haka ne yayin taron manema labarai, yana mai cewa, Sin da Afirka abokan juna ne na kwarai na dogon lokaci komai wahala ko dadi. A lokacin da kasar Sin ta shiga lokaci mai tsanani na yaki da COVID-19, kasashen Afirka sun nuna mata goyon baya, kuma kasar Sin ba za ta taba mantawa ba.

Ya ce, kasar Sin tana mayar da hankali kan yanayin cutar a nahiyar Afirka, har ma ta samarwa AU da dukkan kasashen nahiyar da cutar ta bulla a kasashensu taimakon kayayyakin yaki da cutar da ake bukata rukuni-rukuni.(Ibrahim)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China