2020-04-14 11:05:03 cri |
Bisa labarin da aka samu daga taron nemema labarai da majalisar gudanarwar kasar Sin ta kira jiya Litinin a birnin Beijing, an ce, ana daukar tsauraran matakan kandagarki da dakile cutar COVID-19 a fannonin zirga-zirgar sama da ruwa da ma mota, inda ake bukatar tattara dukkan mutane masu neman shigowa kasar Sin daga ketare kuma a killace su har na tsawon kwanaki 14, a kokarin takaita yaduwar cutar daga masu dauke da kwayar cutar, da rigakafin yaduwarta tsakanin masu dauke da ita da masu mu'amala da su, kana da kokarin ganin babu mutanen da za su kamu da cutar sakamakon hulda da wadanda suka yi mu'amala da masu cutar.(Kande Gao)
| ||||
® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China