Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Zhong Nanshan ya zanta da 'yan kasashen waje kan fasahohin yaki da cutar COVID-19 a birnin Guangzhou
2020-04-16 10:15:36        cri
A ranar 15 ga wata, shugaban tawagar manyan masana ta kwamitin kiwon lafiyar kasar Sin, kana kwararren aikin injiniya na kasar Sin Zhong Nanshan ya zanta da 'yan kasashen ketare guda 19 dake aiki ko kuma karatu a birnin Guangzhou, inda ya yi musu bayani kan matakan da kasar Sin ta dauka wajen yin kandagarki da dakile yaduwar cutar numfashi ta COVID-19, da kuma amsa tambayoyin da suka yi masa.

Galibin 'yan kasashen ketare da suka halarci taron su ne daliban dake karatu a binrin Guangzhou, wasu kuma suna aiki a birnin, wadanda suka zo daga kasashen Japan, Australia, Somaliya, Nijeriya, Malawi da kuma Ghana da sauransu.

A yayin zantawar tasu, Zhong Nanshan ya yi musu cikakken bayani kan yadda kasar Sin take yaki da cutar numfashi ta COVID-19. Ya ce, kasar Sin ta dauki matakai masu karfi, kamar killace birane, gabatar da bayanai ga al'umma ba tare da boye kome ba, da kuma kafa tsarin hadin gwiwar yin kandagarki da dalike yaduwar annobar, domin hana yaduwar cutar numfashi ta COVID-19 a kasar baki daya.

Haka kuma, ya ce, barkewar annobar ya zama darasi ga dukkanin kasashen duniya, ya kamata mu kara saninmu game da duniyar da muke zama cikinta, da kuma yin hadin gwiwa wajen yaki da cutar. (Maryam)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China