Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Yadda Amurka ta dakatar da ba da kudaden da take baiwa WHO ya lalata muradunta da na kasashen duniya
2020-04-15 22:17:26        cri

A jiya Laraba, shugaban kasar Amurka ya sanar da dakatar da kason kudaden da kasarsa ke baiwa hukumar lafiya ta duniya(WHO), tare da zargin hukumar da yin sakaci da aikin tinkarar cutar numfashi ta COVID-19, abin da a cewarsa ya haifar da barkewar cutar a fadin duniya.

Tun bayan bullar cutar, kasancewarta hukuma mai fada a ji a fannin kiwon lafiyar duniya, WHO ta taka rawar gani a bangaren inganta hadin gwiwar kasa da kasa wajen yakar cutar. A daidai lokacin da yawan wadanda suka harbu da cutar ya kai kusan miliyan biyu a duniya, yadda Amurka ta yanke shawarar dakatar da biyan kason kudaden da take baiwa WHO ba kawai saba alkawarin da ta yi ba ne, haka ya kuma lalata hadin gwiwar da kasashen duniya ke yi a kokarinsu na shawo kan cutar, har ma zai lalata kokarin da hukumar WHO ke yi na samar da gudummawa ga kasashe masu tasowa.

A yau Laraba, Mr.Bill Gates, mai kamfanin Microsoft, ya bayyana a kafar sada zumunta cewa, matakin da Amurka ta dauka hadari ne sosai. Ya ce, WHO na dakile saurin yaduwar cutar bisa ayyukan da take gudanarwa, kuma yanzu ne kasa da kasa suke bukatar hukumar fiye da kowane lokaci.

Da ma tuni alamu sun nuna aniyar Amurka, ta dakatar da biyan kason kudin da take baiwa hukumar. Ya zuwa ranar 29 ga watan Faburairun da ya wuce, Amurka ba ta biya sama da kaso 70% na kudin karo-karo da ya kamata ta baiwa WHO a shekarar 2019 a matsayinta na mambar hukumar ba, sannan kuma ba ta biya ko da sisin kobo ba na karo-karon shekarar 2020 da ya kamata ta biya kafin ranar 1 ga watan Janairun wannan shekara.

Wannan mataki na Amurka, ba komai ba ne illa neman shafawa wasu kashin kaji, don ta fake kan mummunan kuskuren da ta aikata a daidai lokacin da ake fuskantar matsanancin hali na yaki da cutar.(Lubabatu)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China