Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Mike Pompeo yana zubar da kimar Amurka
2020-04-13 21:05:56        cri

A yayin da ake kokarin dakile yaduwar cutar mashako ta COVID-19 a duk fadin duniya, Amurka na kara bata sunan wasu kasashe, al'amarin da ya ci gaba da zubar da kimar kasar.

Ga wasu abubuwan da Amurka ta yi kwanan nan a lokacin da kasashen duniya suka himmatu wajen yakar cutar: Ta kwace abubuwan rufe baki da hanci a kan hanyarsu ta zuwa kasar Jamus. Ta kuma umurci kamfanin 3M ya dakatar da fitar da abubuwan rufe baki da hanci zuwa kasashen Kanada da sauran wasu kasashen dake Latin Amurka. Har wa yau, ba sau daya ba kuma ba sau biyu ba Amurka ta dorawa kasar Sin laifin rashin daukar kwararan matakan tinkarar cutar, da kalaman da ya shafi kabilanci. Bugu da kari, Amurka ta kara sanyawa Iran da Cuba takunkumi, abun da ya sa suka gaza samun isassun kayayyakin jinya da suke bukata.

Yanzu ana kara samun mutanen da suka dorawa sakataren harkokin wajen Amurka Mike Pompeo laifin cewa, shi ne ya haddasa raguwar da'a ta Amurka a bangaren harkokin diflomasiyya. Har ma Jaridar Washington Post ta wallafa wani sharhi, inda ta bayyana cewa, gazawar Pompeo a fannin shawo kan annobar COVID-19, ya sa ya zama daya cikin sakatarorin harkokin waje mafi muni a tarihin kasar ta Amurka.

Mike Pompeo, tamkar dan amshin shatan shugaban Amurka Donald Trump ne, wanda ke yunkurin yin amfani da wayonsa domin sauya manufofin fadar White House ta bangaren tsaron kasa, da jagorantar jami'an diflomasiyyar kasar su kara bin ra'ayin nuna bangaranci. Duk da cewa yana biyan bukatunsa na siyasa, harkokin diflomasiyyar Amurka na ci gaba da tabarbarewa, har ma kimar shugabannin Amurka yana zubewa a fadin duniya baki daya.(Murtala Zhang)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China