Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Me Zargin Da Gwamnatin Kasar Amurka Ta Yiwa Kafofin Watsa Labarai Ke Nunawa
2020-04-15 16:52:33        cri
"Ba ki da kunya kina fadin haka!" "Kin san labarin karya ne kike fada, har hukumar da kuke wa aiki tana fitar da labarai na karya"……

A ranar 13 ga wata, yayin taron manema labaran da aka kira a fadar White House, shugaban kasar Amurka ya sake fusata kan tambayar da 'yar jaridar Gidan Rediyon Columbia ta yi masa, inda ta nuna shakku kan ko gwamnatin kasar Amurka game ta gudanar da ayyukanta yadda ya kamata a watan Fabrairun bana.

Cikin 'yan kwanankin nan, shugaban kasar Amurka ya ci gaba da zargin 'yan jaridun kafofin watsa labaran kasar, amma abun tambaya shi ne, ko mene ne dalilin da ya sa yake fushi haka, bari mu dubi misali daga jaridar The New York Times.

Kwanan baya, jaridar The New York Times ta fidda wani sharhi mai taken "Nazari kan jerin kwayoyin dabi'ar mutane: galibin kwayoyin cutar numfashi ta COVID-19 na birnin New York sun zo ne daga kasashen Turai", inda ake zaton cewa, galibin kwayoyin cutar numfashi ta COVID-19 a birnin New York sun zo ne daga masu yawon shakatawar kasashen Turai, kuma cikin sharhin, an ce, kasar Amurka tana iya gano cutar da sauri, idan da ta yi bincike kan cutar cikin himma da kwazo. A karshe dai, shugabannin kasashen Amurka, sun yi Allah wadai da wannan sharhi da kakkausan harshe.

Amma, in mun kalli wannan sharhi, za mu gane cewa, jaridar The New York Times, ta ruwaito ra'ayoyi na masanan da abun ya shafa da dama, har ta fadi cikkakun sunayensu, bayanin da ta yi cikin wannan sharhi suna kuma da inganci sosai.

Kafin haka kuma, gwamnatin kasar Amurka ta zargin Muryar Amurka wato VOA da cewa, ta kashe kudaden 'yan kasar Amurka wajen tallafawa kasar Sin. Mun san cewa, gwamnatin kasar Amurka ita ce ta samar da kudi ga VOA, kuma VOA ya yi kokarin kunna wutar kiyayya ga kasar Sin, da kuma fidda labarai masu bata sunan kasar Sin.

Amma, a ranar 8 ga wata, lokacin da aka bude birnin Wuhan, VOA ya fidda wani labari, inda ya nuna yabo ga kasar Sin, dangane da matakan killace birnin Wuhan da ta dauka, ya ce, wannan abin koyi ne ga kasa da kasa. Kuma a karon farko, VOA ya fadi gaskiya game da kasar Sin, sa'an nan, gwamnatin kasar Amurka ta fara zargin kafar ta VOA, lamarin da ya nuna anihin VOA, da kuma karyar da gwmnatin kasar Amurka take yi ta fuskar 'yancin Magana.

Kuma, mun gane cewa, abin da ya fusata gwamnatin Amurka ba karya ba ce, kawai dai batu ne na siyasa. A ganin gwamnatin kasar Amurka, nuna zargi ga kasar Sin, shi ne kawai daidai, kuma nuna amincewa kan kasar Sin, zai zama tallafawa kasar Sin. Kaman a lokacin farkon barkewar cutar numfashi ta COVID-19, jaridar The New York Times ta ce, birnin Wuhan shi ne asalin cutar numfashi ta COVID-19, gwamnatin kasar Amurka ba ta fadi komai kan wannan batu ba. Amma a lokacin da ta ruwaito maganar masana cewa, cutar ta shiga kasar Amurka daga Turai ne, gwamnatin kasar Amurka ta ce, wannan labari ne na karya.

Bambancin da kasar Amurka ta nuna, ya shaida cewa, manufar 'yancin magana dabara ce kawai ta siyasa ta gwamnatin kasar Amurka. Shi ya sa, jaridar The Washington Post ta ce, a ganin gwamnatin kasar Amurka, ma'anar labari na karya, shi ne labari na gaskiya, muddin dai ya bata sunan shugaban kasar Amurka. (Mai Fassarawa: Maryam Yang)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China