Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Mike Pompeo ya kara kuskure kan da'a da adalci na Amurka
2020-04-12 21:30:49        cri

Ya zuwa tsakiyar ranar 11 ga wata bisa agogon wurin, adadin wadanda suka kamu da cutar numfashi ta COVID-19 a kasar Iran ya kai 70029, ciki kuwa wadanda suka rasa rayukansu sun kai 4357, yawan mutanen da suka mutu ya wuce matsakaicin adadin na duk duniya. Jami'in hukumar lafiya ta kasar ya bayyana cewa, muhimmin dalilin da ya sa aka samu mace-mace mai yawa shi ne karancin kayan lafiya duba da irin takunkumin da Amurka ta sanyawa kasar.

A wannan muhimmin lokacin da kasar Iran ke dakile cutar, sakataren harkokin wajen kasar Amurka Mike Pompeo sau da dama ya bayyana cewa, ba za a soke takunkumi kan Iran ba, hakan ya kara tsanantar halin da Iran ke ciki, kuma matakin ya sabawa ra'ayin jin kai. Ba kawai zai kawo mugun tasiri ga ayyukan yakar cutar na Iran ba, har ma zai kawo cikas ga ayyukan hadin kai na hana yaduwar annobar a duniya baki daya.

Game da haka, kasashen duniya sun yi kira ga kasar Amurka da ta soke takunkumin da ta sakawa wasu kasashe, ciki har da Iran. Amma, Mike Pompeo bai amince da hakan ba, bisa dalilinsa na cewa wai "kamata ya yi a san cewa, babu takunkumin da zai iya hana tallafin jin kai, da kayayyakin aikin jinya da kuma magunguna su shiga kasar Iran ba." Amma, rahoton da wata hukumar kare hakkin bil Adama ta bayar a bana, ya nuna cewa, "takunkumin ya hana bankuna da kamfanoni na kasa da kasa su yi mu'amalar kasuwanci da ta kudi tare da kamfanonin kasar Iran, ciki har da cinikayyar jin kai."

Jaridar The Washington Post ta nuna cewa, Mike Pompeo ya maida yanayin annobar a matsayin hanyar karfafa matsin lamba. A nata bangaren, jaridar The New York Times tana ganin cewa, wasu 'yan siyasar Amurka sun maida cutar kamar wata damar tilastawa Iran mika wuya ga Amurka har ma da tabbatar da mika mulkin kasar. (Bilkisu Xin)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China