Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Me ya sa Pompeo ke son zama ministan harkokin wajen Amurka mafi nuna rashin kwarewa a tarihi
2020-04-13 13:02:25        cri

Kwanan baya, jaridar "The Washington Post" ta Amurka, ta bayyana Mike Pompeo a matsayin daya daga cikin ministocin harkokin wajen Amurka mafiya nuna rashin kwarewa a tarihi, sakamakon matakan da ya dauka lokacin da ake tsaka da yaki da cutar COVID-19.

Laifuffuka biyu da jaridar ta bayyana game da Mike Pompeo su ne, daukar matakai marasa ma'ana na kaiwa kasar Sin hari, wadanda ba su da amfani a yaki da wannan mummunar cutar, kana kuma Pompeo ya kara matsa lamba kan kasar Iran, ta hanyar hana sufurin kayayyaki zuwa kasar, yayin da cuta ta dabaibaye dukkanin duniya, duk da cewa abokan kawancenta ciki har Birtaniya, sun yi kira ga Amurka da ta daina yin hakan, matakin da ya sanya mutanen Iran har miliyan 80 cikin matukar mawuyancin hali, wanda zai sa su rasa rayukansu, saboda karancin kayayyakin jin kai.

Ya zuwa yanzu, yawan Amurkawa da suka kamu da wannan cuta ya kai fiye da dubu 500, kana yawan mamata shi ma ya haura dubu 20, adadin da ya nuna cewa, Amurka ta zama kasa dake da yawan mamata a duniya a gabanin cutar. A sa'i daya kuma, jihohi 50 na kasar a karo na farko, dukkansu sun shiga halin tinkarar bala'i mafi tsanani a tarihin su.

Maganar da Pompeo ke yi kan kasar Sin a lokacin cutar duk bisa wannan tunani ne, wato bata sunan kasar Sin, da mayar da fari baki, da kuma jirkita gaskiya.

Burinsa shi ne tayar da hankalin Amurkawa, don su nuna kiyayya ga kasar Sin, ta yadda zai iya dauke hankalin Amurkawa daga gwamnatin Amurka.

Ban da wannan kuma, sau da dama Mike Pompeo ya sanar da ci gaba da takunkumin da kasar ke yiwa Iran, abin da ya jefa kasar Iran cikin hali mafi wuya, matakin da ya sabawa tunanin jin kai.

Hakikanin gaskiya dai Amurka, tana neman cimma burinta a siyasance ne. Jaridar New York Times na ganin cewa, wasu 'yan siyasa na Amurka sun mai da wannan cuta, wata dama mai kyau wajen tinkarar Iran, tare da sanya takunkumin da ke kan ta, don tilasta mata ta mika wuya ga Amurka, har ma kaiwa ga hambarar da mulkinta.

Mai nazari na kwalejin nazarin raya da tsare-tsaren kasar na Jami'ar Jama'ar kasar Sin Diao Daming ya nuna cewa, mambobin gwamnatin kasar Amurka dake da alaka da batun tsaro, na matukar son tayar da hankalin Amurkawa, bisa bayyana cewa, wai akwai kalubaloli daga kasashen waje, da nufin nuna ma'anar kasancewarsu, da samun karin kasafin kudinsu.

Wasu kungiyoyi karkashin gwamnati na son cimma moriyarsu, abin da ya sa suna daukar matakan tsaro, da cinikayya da dai sauransu, bisa burinsu yadda suke so, inda suke yin biris da muradun jama'ar Amurkawa. (Amina Xu)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China