Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Surutun banza na 'yan siyasar Amurka ba su iya boye kurakurai uku da suka yi wajen yaki da cutar COVID-19 ba
2020-04-14 13:05:31        cri

Yayin da ake kara samun yawan mutanen da suke kamuwa da cutar COVID-19, da kuma wadanda suke mutuwa a sakamakon cutar a kasar Amurka, 'yan siyasar kasar suna kara furta zargin kasar Sin game da yaduwar wannan annoba.

Bi da bi, irin wadannan 'yan siyasa sun yi ta zargin kasar Sin ba tare da wani dalili ba, kamar su furta kalmar "cutar COVID-19 ta fito daga kasar Sin", da "Sin ta boye bayanai game da cutar", yayin da wasu ke cewa ya kamata Sin ta dauki alhakin yaduwar cutar a dukan duniya, har ma suna saka kimi ga wasu hukumomi, ko kungiyoyi, da su nemi diyya daga kasar Sin.

Amma ana iya ganin hakikanin yanayin da ake ciki. Kasa da kasa ciki har da hukumar kiwon lafiya ta duniya wato WHO, sun riga sun yabawa Sin bisa iya kokarinta na yaki da cutar COVID-19. Don haka 'yan siyasar kasar Amurka sun yi magana maras tushe, wadda ba ta iya cutar da kasa da kasa, kana ba za ta boye kuskurensu wajen yaki da cutar ba.

Bisa dalilai uku, wato irin wadannan 'yan siyasa sun gaza yaki da cutar har na tsawon watanni biyu domin ba su mai da hankali kan batun ba, kana sun gaza yin kokarin yaki da cutar, domin hamayyar dake tsakanin jam'iyyun kasar, kana sun kuma gaza yin hadin gwiwa wajen yaki da cutar da sauran kasashen duniya bisa ka'idar maida Amurka a matsayin gaban komai.

"Cuta ba ta nuna kabilanci da wariya ba, kowa na fuskantar hadarin." Wannan gargadi ne da mujallar "Nature" ta bayyana wa duk duniya a lokacin da take neman afuwa daga kasar Sin. Kurakuran da kasar Amurka ta yi sau da dama wajen yaki da cutar sun shaida cewa, masu tsara manufofi na Washington na kasar Amurka ba su fahimci wannan gargadi ba, ba su mai da hankali kan ceton rayukan jama'a ba, don haka wannan ya sa suka daidaita matsalar yaki da cutar ta hanyar yin kurakurai da dama. (Zainab)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China