Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Najeriya na kara azamar tunkarar cutar COVID-19
2020-04-14 10:29:52        cri

Ministan lafiya na tarayyar Najeriya Osagie Ehanire, ya ce gwamnatin na kara azama wajen tunkarar cutar numfashi ta COVID-19, a wani mataki na tabbatar da dakile yaduwar ta cikin kasar.

Wata sanarwa da ofishin ministan ya fitar a jiya Litinin, ta bayyana cewa, gwamnati ta fara gudanar da rangadi na wuraren da aka tanada, domin yaki da cutar na gwamnati, da na masu zaman kansu dake sassan jihohin kasar, inda aka fara da jihohin da cutar ta fi yaduwa a cikin su.

Hakan a cewarsa ya dace da cikakken tsaren dakile bazuwar cututtuka da aka sani. Kaza lika matakin zai ba da damar fadada yawan gadajen killace masu fama da cutar da ake da su, da kare lafiyar jami'an lafiya a dukkanin sassan kasar.

Mr. Osagie Ehanire ya kara da cewa, aikin fadada yawan gadajen kwantar da masu dauke da cutar zai fara ne da asibitocin birnin Abuja fadar mulkin kasar, yayin da tuni asibitin koyarwa na jami'ar birnin Lagos ya samar da gadaje 60, a cibiyar sa ta kebe masu fama da cutar.

Ya ce cibiyar hana yaduwar cututtuka ta kasar ko NCDC a takaice, za ta ci gaba da bunkasa ayyukanta na gwajin cutar ta COVID-19, kuma kawo yanzu, an tanaji dakunan gwajin cutar 9 a sassan kasar daban daban.

Ministan lafiyar ya kuma jaddada cewa, NCDC za ta ci gaba da goyon bayan ayyukan tunkara, da zama cikin shiri, domin yaki da wannan annoba a dukkanin jihohin kasar, inda za a tura tawagar jami'ai ta gaggawa a duk inda aka samu bullar cutar, cibiyar za ta kuma fadada binciko wadanda suka yi cudanya da masu dauke da cutar, da ba da kulawa ga masu dauke da ita, da samar da bayanai masu nasaba, da inganta ayyukan kandagarki da na shawo kan cutar. (Saminu)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China