Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Yan sandan Najeriya sun damke mutane 18 da aka zargi da yin garkuwa a tsakiyar kasar
2020-04-13 10:02:16        cri
Kimanin mutane 18 da ake zargin musu yin garkuwa da mutane ne suka shiga komar 'yan sandan Najeriya a jihar Nasarawa dake shiyyar tsakiyar kasar, wani jami'in 'yan sandan yankin ya tabbatar da hakan a ranar Lahadi.

Uku daga cikin mutanen da ake zargin sun samu harbin bindiga a lokacin da aka yi musayar wuta tsakaninsu da jami'an tsaron, a cewar Bola Longe, babban jami'in 'yan sandan jihar Nasarawa.

A cewar Longe, ana tuhumar mutanen da aikata laifuffuka daban daban da suka shafi yin garkuwa da mutane a fadin jihar.

Jami'in ya ce, tuni mutanen da aka kubutar daga hannun masu garkuwar sun riga sun koma cikin iyalansu, an yi nasarar kubutar da su ne bayan samun wasu bayanan sirri game da ayyukan masu garkuwar.(Ahmad Fagam)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China