Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Dakarun tsaron Najeriya sun kubutar mutane 7 da aka yi garkuwa da su
2020-04-13 09:51:06        cri
Helkwatar tsaron Najeriya ta sanar a ranar Lahadi cewa, sojojin kasar sun yi nasarar kubutar da mutane 7 da masu garkuwa suka yi awon gaba da su yayin wani samame da dakarun tsaron suka kaddamar.

A sanarwar da John Enenche, kakakin rundunar tsaron Najeriya ya fitar, ya ce dakarun sun kaddamar da samamen ne a ranar Lahadi a yankunan jihar Naija.

Eneche ya ce, 'yan bindigar sun tsere, inda suka bar mutanen da suka yi garkuwar da su bayan mummunan musayar wuta da suka yi da dakarun tsaron kasar.

A cewar kakakin rundunar tsaron, an yi garkuwa da mutanen ne tun a ranar 27 ga watan Maris, inda suke tsare da su a wani waje da ba'a tantance ba a shiyyar tsakiyar Najeriya.(Ahmad Fagam)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China