Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Nijeriya ta amince da rage yawan man da take samarwa
2020-04-14 10:43:02        cri

Nijeriya ta bi sahun takwarorinta na kungiyar kasashe masu arzikin man fetur ta OPEC wajen fara aiwatar da yarjejeniyar da aka cimma ta rage yawan man da suke samarwa, bayan sun ware kasar Mexico.

Wata sanarwa da karamin ministan mai na kasar Timipre Marlin Sylva ya fitar a jiya, ta ce kamar yadda aka amince, Nijeriya za ta bi sahun kasashen OPEC, wajen rage yawan man da suke samarwa da ganga miliyan 9.7 a kowacce rana, tsakanin watan Mayu zuwa Yuni, sannan a rage ganga miliyan 8 a kowacce rana daga watan Yuli zuwa Disamban bana da kuma ganga miliyan 6 a kowacce rana daga watan Junairu 2021 zuwa Afrilun 2022.

Ya ce yarjejeniyar ta OPEC ba ta shafi yawan daskararren mai da ake samarwa ba, inda yawansa ya tsaya kan ganga dubu 360 zuwa dubu 460 a kowacce rana.

Ministan ya ce matakin zai ba da damar daidaita kasuwar mai ta duniya, sannan ana sa ran ya farfado da farashin man zuwa dala 15 kan kowacce ganga cikin gajeren lokaci.

Har ila yau, ya ce zai daidaita kasafin kudin kasar na shekarar 2020 da ya yi hasashen farashin mai a dala 30 kan kowacce ganga. (Fa'iza Mustapha)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China