Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Dakarun sojin Najeriya sun hallaka 'yan bindiga a kalla 10 a Sokoto da Zamfara
2020-04-13 09:12:46        cri
Rundunar sojojin Najeriya ta ce, ta yi nasarar hallaka a kalla 'yan bindiga 10, yayin wani simame da dakarunta suka gudanar a jihohin Sokoto da Zamfara, dake arewa maso yammacin kasar a ranar Asabar din karshen mako.

Cikin wata sanarwa da kamfanin dillancin labarai na Xinhua ya samu kwafinta a birnin Abuja, rundunar sojin kasar ta ce, yayin hare haren da ta kaddamar kan wasu maboyar 'yan bindigar dake jihohin biyu, ta samu nasarar kubutar da mutane 18 da 'yan bindigar ke garkuwa da su, da suka hada da maza 10, da mata 4, da kananan yara 4.

Kaza lika sojojin sun cafke wani da ake zargin shi ne ke samarwa 'yan bindigar bindigogi a jihar Sokoto. (Saminu)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China