Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Yawan wadanda suka kamu da COVID-19 a Najeriya ya karu zuwa 323
2020-04-13 20:05:19        cri
Cibiyar hana yaduwar cututtuka a Najeriya (NCDC) ta sanar da cewa, yawan wadanda suka kamu da cutar numfashi ta COVID-19 a kasar ya karu zuwa 323, bayan samun rahoton sabbin mutane 5 da suka kamu da cutar.

A bayanan da ta ke fitarwa game da yanayin cutar, cibiyar ta ce mutane 10 sun mutu a kasar dake yammacin Afirka sanadiyyar cutar. Haka kuma galibin wadanda suka kamu da cutar na samun sauki. Kana daga cikin marasa lafiya da ake yiwa jinya a asibitoci daban-daban dake kasar, mutane 85 sun warke har an sallame su.

Har yanzu dai Lagos, dake zama cibiyar kasuwancin kasar, nan ne inda cutar ta fi Kamari inda mutane 176 suka kamu da cutar, yayin da Abuja, fadar mulkin kasar ke da mutane 56 da cutar ta harba.(Ibrahim)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China