Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Rundunar 'yan sandan Najeriya ta tura dakarun musamman domin dakile ayyukan bata gari yayin da ake tsaka da yaki da COVID-19
2020-04-15 10:53:20        cri

Babban sifeton 'yan sandan Najeriya Mohammed Adamu, ya ba da umarnin tura dakaru na musamman, domin dakile ayyukan bata gari a jihohin Lagos da Ogun, yayin da ake tsaka da aiwatar da dokar zaman gida, a yakin da kasar ke yi da cutar numfashi ta COVID-19.

Da yake tabbatar da hakan cikin wata sanarwa, kakakin rundunar Frank Mba, ya ce wannan mataki zai karfafa tsaro, da karfin gwiwar al'umma a yankunan wadannan jihohi da suka fuskanci tashe tashen hankula.

Mr. Mba ta ce mataimakin babban sifeton 'yan sandan kasar mai kula da ayyukan bincike, da tsare tsare ne zai jagoranci ayyukan da rundunar za ta gudanar.

A wani ci gaban kuma, rundunar 'yan sandan ta yi nasarar cafke wasu bata gari su 191, da ake zarginsu na cikin gungun wasu matasa da suka rika aikata masha'a, a titunan wasu unguwannin jihohin Lagos da Ogun.

An kama mutanen ne dauke da bindigogi kirar hannu 15, da albarusai 52, da adduna da gatari 42, da kunshi mai yawa na wani abu da ake kyautata zaton tabar wiwi ce. (Saminu)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China