Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Yawan wadanda suka kamu da COVID-19 a Najeriya ya karu zuwa 343
2020-04-14 19:35:49        cri
Cibiyar hana yaduwar cututtuka a Najeriya (NCDC) ta sanar da cewa, yawan mutanen da aka tabbatar sun kamu da cutar COVID-19 a kasar ya karu zuwa 343.

Cibiyar ta bayyana cikin wata sanarwa da kamfanin dillancin labarai na Xinhua ya samu kwafenta a yau Talata cewa, ya zuwa jiya Litinin, an samu sabbin mutane 20 da aka tabbatar sun kamu da cutar a jihohi biyar na kasar.

Sai dai cibiyar ta bayyana cewa, galibin mutane 343 da suka kamu da cutar a kasar, suna samun sauki. Daga cikin wannan adadi, an sallami mutane 91 bayan sun warke daga cutar, kana mutane 10 sun mutu. (Ibrahim)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China