Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Najeriya ta tsawaita dokar zaman gida da mako 2 a manyan biranen kasar
2020-04-15 10:16:09        cri
Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya tsawaita wa'adin dokar kulle da mako biyu a babban birnin kasar Abuja da Lagos, cibiyar kasuwancin kasar.

A jawabin da shugaban kasar ya gabatar kai tsaye ta kafafen yada labaran kasar da yammacin ranar Litinin, wanda shi ne jawabinsa na biyu tun bayan barkewar annobar a kasar mafi yawan jama'a a nahiyar Afrika, shugaban Buhari ya kuma tsawaita dokar hana zirga zirgar a jihar Ogun, mai yawan masana'antu dake shiyyar kudu maso yammacin Najeriya, na tsawon makonni biyu.

"Mun yanke wannan hukunci mai tsanani wanda zai yi matukar shafar yanayin rayuwar jama'a, kana zai jefa rayuwar mutane cikin kunci, ga iyalai da al'ummomin yankuna," in ji shugaban kasar.

Shugaban Najeriya ya ce, wannan sadaukarwa ce da ake bukata domin dakile yaduwar annobar COVID-19 a kasar. Daukar matakin ya zama tilas domin ceton rayuwar jama'a.

Tun da farko a ranar 30 ga watan Maris, Najeriyar ta ayyana dokar zaman gida ta tsawon makonni biyu a manyan biranen kasar uku da suka hada da birnin tarayya Abuja da Lagos, da kuma Ogun.(Ahamd Fagam)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China