Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
IMF ya yi hasashen farfadowar tattalin arzikin Sin a rubu'i na biyu na bana
2020-02-23 15:53:39        cri
Manajar daraktar gudanarwar asusun bada lamini na duniya (IMF), Kristalina Georgieva ta sanar a jiya Asabar cewa tana tsammanin tattalin arzikin kasar Sin zai iya komawa daidai a rubu'i na biyu na wannan shekara ta 2020.

Georgieva ta ce, ta yi kyakkyawar tattaunawa da jami'an kasar Sin, a cewarta, huhumomin kasar Sin suna aiki tukuru wajen daukar matakan rage illolin da cutar numfashi ta COVID-19 za ta iya haifarwa ga tattalin arzikin kasar.

Ta ce, bisa ga irin tanade-tanaden da aka yi idan an kammala aiwatar da su tattalin arzikin kasar Sin zai iya daidaituwa a rubu'i na biyu na bana.

Georgieva ta fada a lokacin taron ministocin kudi da shugabannin manyan bankunan kasashen G20 cewa, a bisa wannan sakamako, tasirin da matsalar za ta yi ga tattalin arzikin duniya ba ta da girma sosai kuma na gajeren lokaci ne. (Ahmad Fagam)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China