Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
AU ta lashi takobin kara himmantuwa wajen tabbatar da daidaiton jinsi a Afrika
2020-03-09 10:15:45        cri
Yayin da ake bikin ranar mata ta duniya, Tarayyar Afrika AU, ta jaddada kudurinta na kara zage damtse wajen tabbatar da daidaiton jinsi a nahiyar Afrika.

Cikin wata sanarwa da aka fitar a jiya, shugaban hukumar tarayyar, Mousa Faki Mahamat, ya ce AU ta himmantu wajen cimma daidaiton jinsi da tabbatar da mata da maza na samun damarmaki iri daya.

Yayin taron shugabannin kasashe mambobin tarayyar da aka kammala a baya bayan nan a Addis Ababan Habasha, shugabannin sun ayyana shekarun 2020 zuwa 2030, a matsayin karnin shigar da mata cikin harkokin tattalin arziki da na hada-hadar kudi a nahiyar.

Tarayyar Afrika da hadin gwiwar hukumar kula da tattalin arzikin Afrika ta MDD, sun kaddamar da wani asusun raya harkokin mata, da nufin samar da abubuwan da ake bukata daga bangarori masu zaman kansu na duniya, domin samar da kudi ga shirye-shiryen mata da inganta samar da kyakkywan yanayin domin kara damawa da su a fadin nahiyar.

Mousa Faki Mahamat, ya kara da cewa, AU za ta ci gaba da jajircewa wajen kawo karshen cin zarafin mata da 'yan mata da dukkan illolinsu, tare da kare 'yan mata daga dukkan nau'ikan cin zarafi; ciki har da auren wuri da wasu al'adun gargajiya masu lahani. (Fa'iza Mustapha)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China