Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Daraktan NCDC: Fasahohi da dabarun Sin na yakar COVID-19 na da babbar ma'ana ga Najeriya
2020-04-10 11:22:34        cri

Jiya Alhamsi, jaridar Daily Trust ta Najeriya ta wallafa zantawarta da daraktan cibiyar kandagarkin cututtuka ta Najeriya Chikwe Ihekweazu, game da tawagar yaki da COVID-19 ta CRCC da ta isa Najeriya a kwanan baya. Chikwe Ihekweazu ya ce, matakin da gwamnatin kasar Sin ke dauka na da amfani matuka wajen hana yaduwar cutar, kuma kamata ya yi Najeriya ta koyi fasahohi da dabarun kasar Sin. Ya ce zuwan tawagar yaki da cutar ta kamfanin CRCC Najeriya a wannan lokaci na da babbar ma'ana, domin za ta gabatar da fasahohin kasar Sin ga Najeriya tare kuma da kai dimbin kayayyakin jiyya da ake matukar bukata a kasar, kuma Najeriya na maraba da su kwarai da gaske. Yanzu ba lokacin baza jita-jita ko makarkashiya ba ne. Wannan mumunar cuta ta nuna cewa, dole ne kasa da kasa su hada kansu, domin wannan ce hanya daya tilo ta yakar cutar da cimma nasara. (Amina Xu)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China