Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Tawagar ma'aikatan lafiyar kasar Sin ta isa Najeriya da kayayyakin aiki
2020-04-10 20:34:42        cri
A jiya ne, wata tawagar ma'aikatan lafiya mai mutum 15 da wani kamfanin kasar Sin ya kafa ta isa Abuja, fadar mulkin kasar da tarin kayayyakin yaki da COVID-19, bisa bukatar gwamnatin kasar Najeriya.

Mai magana da yawun ma'aikatar harkokin wajen kasar Sin Zhao Lijian, shi ne ya bayyana haka yayin da yake amsa tambayoyin manema labarai. Ya ce, baya ga ma'aikatan lafiyar, akwai wasu daga cikin ma'aikatan kamfanin a cikin jirgin da ya dauko su zuwa Najeriya.

Zhao ya kara da cewa, a shirye kasarsa take ta taimakawa sauran kasashen Afirka, ciki har da Najeriya, ta yadda za su hada hannu don ganin bayan wannan annoba.

A nasa jawabi, ministan lafiya na Najeriya, ya ce taimako da goyon bayan da gwamnatin kasar da ma kamfanonin kasar Sin suke baiwa Najeriya, ya zo a kan lokaci, ya kuma taimaka wajen magance bukatun gaggawa na kandagarki da hana yaduwar cutar, da kara imanin bangaren Najeriya a yakin da take yi da wannan cuta. (Ibrahim)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China