Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Shugaba Xi ya jadadda muhimmancin shawo kan COVID-19 wajen samun nasarar fatattakar talauci
2020-03-07 16:21:03        cri
Shugaban kasar Sin, Xi Jinping, ya jaddada bukatar shawo kan tasirin cutar COVID-19 wajen cimma nasarar fatattakar talauci.

Xi Jinping, wanda shi ne Sakatare Janar na kwamitin koli na JKS, kuma shugaban kwamitin kolin rundunar sojin kasar, ya bayyana haka ne yayin wani taron karawa juna sani kan hanyar samun nasarar yaki da fatara.

Shugaban ya jaddada cewa, fitar da mazauna karkara da yanzu haka cikin talauci daga wannan kangi a bana, alkawari ne da kwamitin koli na JKS ta dauka, kuma dole a cika akan lokaci.

Da yake bayyana taron a matsayin irinsa mafi girma da aka yi tun bayan babban taron wakilan jam'iyyar karo na 18, shugaba Xi ya ce babban aikinsa shi ne, tattaro dukkan abun da ake bukata wajen cin nasarar yaki da fatara, da tabbatar da an cimma mizanin kawar da fatara kamar yadda aka tsara, domin gina al'umma mai matsakaiciyar ci gaba a kowanne fanni. (Fa'iza Mustapha)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China