Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Sin ta lashi takwabin kawar da talauci ta hanyar samar da ayyukan yi
2020-02-25 10:27:59        cri

Mahukuntan kasar Sin sun jaddada kudurinsu na samun nasara kan yakin da suke yi game da kawar da talauci, ta hanyar samar da guraben ayyukan yi ga matalauta, duk da annobar COVID-19 da ta bulla a kasar.

Cikin wata sanarwar hadin gwiwa da ma'aikatar albarkatu da tsaron jama'a da babban ofishin yaki da talauci da raya kasa suka fitar, sun bayyana cewa, ya kamata kananan hukumomi su rika samar da taimako ga wadanda suka rasa ayyukan yi, don hana mutane komawa cikin kangin talauci sakamakon wannan annoba.

Haka kuma, za a tsara yadda ma'aikata 'yan ci rani za su koma bakin aiki ba tare da wata matsala ba, yayin da a hannu guda, su ma kamfanoni da ayyukan noman rani, ya dace su dawo bakin aiki ba tare da bata lokaci ba a yankunan dake da karancin barazanar wannan annoba.

Sanarwar ta kara da cewa, za a baiwa muhimman kamfanoni kudaden alawus-alawus, ta hanyar ba da muhimmanci ga matalauta da aka dauka aiki, sannan za a yiwa leburori matalauta dake aikin wucin gadi kan yaki da wannan annoba rangwame.

Bugu da kari, ya kamata kananan hukumomi, su yiwa leburori matalauta, da ba su bar yankunan karkaka ba jagora, ta yadda za su shirya shiga lokacin hunturu, da sayar da amfanin gona ta kafar Intanet da fitar da amfanin gonansu. Za kuma a samar da horo da rangwamen rayuwar yau da kullum ga matalautan da suke samun horo a yanar gizo, kana wadanda suka rasa aiki sakamakon wannan annoba, za su rika samun tallafin rashin aikin yi. (Ibrahim)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China