Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
An fitar da dukkan gundumomi daga kangin talauci a larduna 8 na daban a kasar Sin
2020-03-02 12:07:01        cri
Rahotanni daga ofishin kula da ayyukan yaki da talauci na majalisar gudanarwar kasar Sin sun ce, ya zuwa karshen watan jiya a bana, an fitar da dukkan gundumomi daga kangin talauci a larduna 8 na daban a kasar Sin, ban da jihar Tibet, wadda ta sanar da fitar da dukkan gudumominta daga talauci a watan Disamban bara.

Ofishin ya jaddada cewa, yanzu an rage yawan mutanen dake fama da talauci, kuma wajibi ne a ci gaba da kokarin taimaka musu. Ya kara da cewa, za a yi iyakacin kokarin kammala ayyukan da suka rage wajen yaki da talauci. Kuma ba za a yi kasa a gwiwa ba, har sai an samu cikakkiyar nasara. (Tasallah Yuan)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China