Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Firaministan Birtaniya ya jaddada ficewar kasarsa daga EU a karshen watan Oktoban bana
2019-09-03 16:24:05        cri

Jiya da dare ne firaministan kasar Birtaniya Boris Johnson ya ba da wata sanarwa bayan taron gaggawa da majalisar ministoci ta kira, inda ya ce, ko ta yaya ba zai bukaci kungiyar tarayyar Turai wato EU ta jinkirta wa'adin ficewar kasarsa daga kungiyar ba. A ranar 31 ga watan Oktoba ne, aka tsara ficewar Birtaniyar daga daga EU.

Firaministan ya yi kira ga 'yan majalisar da su jefa kuri'ar kin amincewa da duk wani yunkuri na jinkirta ficewar kasar daga EU. Haka kuma mista Johnson ya musunta jita-jitar da ake yi cewa, kila zai shirya babban zabe kafin lokacin da aka tsara.(Tasallah)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China