Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Bayan shafe shekaru 47 a matsayin mamba, Birtaniya ta fice daga Tarayyar Turai
2020-02-01 15:59:41        cri
Birtaniya ta fice daga Tarayyar Turai a hukumance da misalin karfe 11 na daren jiya Juma'a agogon GMT, wanda ya kawo karshen shekaru 47 da kasar ta shafe a matsayin mambar kungiyar cinikayya mafi girma a duniya.

Yayin wani jawabin musamman da aka watsa ta talabijin, Firaministan Birtaniya Boris Johnson, wanda ya kama aiki a lokacin da ake tsaka da takaddama kan ficewar kasar daga tarayyar, ya bayyana yanayin a matsayin wani sabon babi.

Boris Johnson ya ce, aikinsu a matsayin gwamnati shi ne hada kan kasar tare da ciyar da ita gaba. Yana mai cewa, abu mafi muhimmanci shi ne fahimtar cewa, yanzu suka fara aiki.

Har ila yau, wannan kuma ya bude babin daddale yarjejeniya da zai kai karshen bana, inda ake sa ran wakilan bangarorin za su fuskanci gwagwarmaya kan cimma yarjejeniyar cinikayya tsakanin Birtaniya da sauran kasashen EU. (Fa'iza Mustapha)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China