Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Jam'iyyun adawa a Birtaniya sun nemi a sake bude majalissar dokoki
2019-09-12 14:14:17        cri
Manyan jam'iyyun adawa na Birtaniya, karkashin jagorancin jam'iyyun Labour Party, da Scottish Nationalist Party, da Liberal Democrats, sun nemi firaministan kasar Boris Johnson, ya sake bude majalissar dokokin kasar.

Gamayyar jam'iyyun sun yi kiran ne a daren jiya Laraba, bayan da wata kotu a yankin Scotland ta yanke hukuncin cewa, matakin rufe majalissar dokokin da firaministan ya aiwatar ya sabawa doka.

A cikin makon gobe ne dai ake fatan daukaka wannan kara gaban kotun koli domin yanke hukunci na karshe. Duk dai da yawan nuna adawa da matakin rufe majalissar dokokin, fadar firaminista Johnson ta nanata cewa, ba za a bude majalissar ba har nan da ranar 14 ga watan Oktoba mai zuwa, sai fa idan kotun koli ce ta ba da umarnin yin hakan. (Saminu)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China