Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Xi: Kasar Sin za ta ci gaba da taimakawa Afirka wajen yaki da COVID-19
2020-04-09 10:20:59        cri

Shugaban kasar Sin Xi Jinping, ya bayyana kudurin kasarsa na ci gaba da taimakawa kasashen Afirka a yakin da suke yi da cutar COVID-19, da kara karfin kasashen nahiyar na kandagarki da hana yaduwar cututtuka.

Shugaba Xi ya bayyana haka ne, jiya Laraba yayin zantawa ta wayar tarho da takwaransa na kasar Afirka ta Kudu Cyril Ramaphosa. Xi ya ce, ya tuna cewa, bayan da cutar COVID-19 ta barke a kasar Sin, gwamnatin Afirka ta kudu da bangarorin al'umma daban-daban na kasar, sun aikowa kasar Sin sakon jaje da goyon baya ta hanyoyi daban-daban.

Xi ya ce, kasar Sin tana goyon bayan kasar Afirka ta kudu a yakin da ta ke yi da COVID-19, kana kasar Sin za ta ci gaba da taimaka mata kamar yadda take bukata gwargwadon karfinta, da raba fasahohinta na kandagarki da hana yaduwar cutar, da karfafa alaka a fannin kiwon lafiya.

Ya kara da cewa, bangaren kasar Sin, yana bibiyar yanayin cutar a Afirka, kuma kasar Sin ta aikawa kungiyar AU rukunin kayayyakin taimako na yaki da cutar da ma kasashen Afirka dake da alaka da kasar Sin.

Haka kuma masana daga sassan biyu, sun gudanar da taro ta kafar bidiyo a lokuta da dama, a hannu guda su ma kamfanonin kasar Sin, da kungiyoyin al'umma da masu zaman kansu, sun samar da taimakon kayayyakin yaki da wannan annoba.

Shugaba Xi, ya ce kasar Sin za ta ci gaba da taimakawa kasashen Afirka, da kara karfin cibiyar hana yaduwar cututtuka ta Afirka, da kara bunkasa alakar Sin da Afirka a fannin kiwon lafiyar jama'a da kandagarki da hana yaduwar cututtuka da taimakawa nahiyar wajen inganta karfinta a wannan fanni.(Ibrahim)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China