Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Ya kamata MDD ta hana wasu kasashe da suke sa ido da tattara sakwanin jama'a ta yanar gizo
2020-03-06 11:55:10        cri
A jiya ne, aka gudanar da tattaunawa game da rahotanni kan batun ikon kare sirrin dan Adam, a yayin taron majalisar kare hakkin dan Adam ta MDD karo na 43, inda wakiliyar musamman ta ma'aikatar harkokin wajen kasar Sin mai kula da hakkin dan Adam Liu Hua, ta bayyana cewa, Sin ta nuna kulawa ga aikin da wasu kasashe suka gudanar na sa ido da tattara sakwanin jama'a, da sabawa ikon mallakar kasa, da kuma keta hakkin dan Adam, musamman ikon kare sirrin dan Adam.

Liu Hua ta bayyana cewa, domin fasahohin sadarwa musamman yanar gizo, suna shafe dukkan duniya, sa ido ga jama'a ta yanar gizo ya keta hakkin dan Adam na jama'ar kasar kanta, da ma sauran kasashen duniya, da kawo illa ga ikon mallakar sauran kasashen duniya, da sabawa ka'idojin tsarin mulkin MDD, kamar su girmama ikon mallakar kasa, da cikakken yankunan kasa, da kuma kaucewa tsoma baki a harkokin cikin gida na kasa da kasa da sauransu. Ya kamata MDD ta dauki matakai don hana kasashen da abun ya shafa, da su sa ido da tattara sakwanin jama'a ta yanar gizo a fadin duniya. (Zainab)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China