Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Guterres ya yi kira da a dauki mataki yayin da WHO ta ayyana COVID-19 a matsayin annobar da ta shafi duniya
2020-03-12 10:08:44        cri
Babban sakataren MDD Antonio Guterres, ya yi kira da a dauki mataki kan cutar numfashi ta COVID-19, bayan da hukumar lafiya ta duniya (WHO) ta ayyana cutar a matsayin wadda ta shafi duniya baki daya.

Guterres wanda ya yi wannan kira cikin wani sako ya ce, matakin da WHO ta dauka a yau, kira ne ga kowa da kowa da kuma dukkan kasashen duniya. Haka kuma kira ne na daukar matakin da ya dace da sadaukar da kai, yayin da MDD da daukacin al'ummar duniya suka hada kai. Amma kuma ya gargadi jama'a da kada su firgita, "Ya kamata mu jajirce a lokacin da muke yaki da kwayar cutar"

A jiya ne dai, babban darektan hukumar lafiya ta duniya, Tedros Adhanom Ghebreyesus ya shaidawa taron manema labarai cewa, WHO ta ce za a iya ayyana cutar COVID-19 da ta barke a matsayin, "Cutar da ta shafi duniya baki daya", ganin yadda cutar ta kara yaduwa a sassan duniya. Ya kuma bukaci kasashen duniya, da su gaggauta daukar managartan matakai don dakile cutar.

Rahoton rana-rana da WHO take fitarwa kan yanayin cutar ya nuna cewa, adadin mutanen da cutar ta halaka a wajen kasar Sin ya zuwa safiyar ranar Laraba, ya kai 1,130, karuwar mutane 258 da cutar ta halaka kan na ranar Talata.

Bayanai na cewa, ya zuwa karfe 10 na safiyar ranar Laraba, agogon tsakiyar Turai, mutane 118,326 ne aka tabbatar cewa, sun kamu da cutar a kasashe da yankuna sama da 110, ciki har da mutane 37,371 da cutar ta kama a wajen kasar Sin.(Ibrahim)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China