Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
MDD na fatan za a gudanar da zabukan majalisun dokoki da na raba gardama lami lafiya a Guinea
2020-03-21 16:05:06        cri
Sakatare Janar na MDD Antonio Guterres, ya bayyana fatan ganin an gudanar da zabukan majalisun dokoki da na raba gardama kan kundin tsarin kasar Guinea da aka shirya yi a gobe, lami lafiya kuma bisa gaskiya.

Wata sanarwar da kakakin MDD Stephane Dujarric ya fitar, ta ce Antonio Guterres na bibiyar yanayin da ake ciki a kasar ta yammacin Afrika, da kuma matakin da shugaba Alpha Conde na kasar ya dauka, na gudanar da zabukan majalisun dokoki da na raba gardama kan kundin tsarin mulkin kasar a gobe Lahadi.

Sakatare Janar din ya yi kira ga dukkan masu ruwa da tsaki su tabbatar an gudanar da sahihin zabe cikin kwanciyar hankali da lumana.

Antonio Guterres, ya jaddada kiran a yi tattaunawa mai ma'ana tsakanin gwamnatin kasar da bangaren adawa da kungiyoyin al'umma, domin cimma matsayar da za ta karbu ga kowa.

Sanarwar ta ce a shirye MDD take ta goyi bayan irin wannan yunkuri, ta hannun manzonta na musamman a yammacin Afrika da yankin Sahel, Mohamed Ibn Chambas.

A jiya Juma'a ne shugaba Conde ya sanar da sabuwar ranar gudanar da zabukan majalisun dokoki da na raba gardama kan kundin tsarin mulkin kasar. Da farko an shirya gudanarwa ne a ranar 16 ga watan Fabreru, wadda aka daga har sau biyu, da farko zuwa 1 ga wata, sannan kuma zuwa gobe 22 ga wata. (Fa'iza Mustapha)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China