Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
An samu karuwar mutane 31 da suka kamu da cutar COVID-19 a babban yankin kasar Sin
2020-04-03 11:50:45        cri
Hukumar kula da lafiya ta kasar Sin, ta ce an samu sabbin masu dauke da cutar numfashi ta COVID-19 su 31, a babban yankin kasar Sin a jiya Alhamis, kuma 29 daga cikin su sun shigo da cutar ne daga ketare.

Kaza lika akwai wasu mutum 2 da suka kamu da cutar a cikin kasar, daya a lardin Liaoning, da wani mutum na daban a lardin Guangdong.

Har ila yau a dai jiyan, mutane 4 sun rasu dukkanin su a lardin Hubei, an kuma samu wasu 12 da ake sanya ido kan su, domin tantance ko suna dauke da cutar ko a'a a babban yankin kasar, dukkanin su kuma sun shigo ne daga waje, kamar dai yadda hukumar lafiyar kasar ta bayyana.(Saminu)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China