Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Sin tana kokarin rage tasirin cutar COVID-19 ta shirin yaki da fatara
2020-04-02 11:16:47        cri

Kasar Sin tana kokarin rage tasirin radadin annobar COVID-19 ta hanyar shirinta na yaki da fatara, kana ta sha alwashin cimma nasarar kammala shirin yaki da fatara na kasar nan da karshen wannan shekara.

Wang Chunyan, jami'in ofishin kula da shirin yaki da fatara da raya cigaba na majalisar gudanarwar kasar Sin, ya fadawa taron manema labarai cewa, kasar Sin tana cigaba da kokarin shawo kan manyan kalubalolin da annobar COVID-19 ta haifarwa shirin yaki da fatara na kasar, yayin da hukumomin gwamnatin kasar suke cigaba da sanya ido ga kananan hukumomin kasar game da yadda ake aiwatar da shirye-shiryen saukaka fatara a fadin kasar.

Domin rage tasirin, gwamnatin Sin ta umarci kamafanoni da sassan hukumomin gwamnati dasu sayi amfanin gonar dake hannun talakawa mazauna karkara, a matsayin wani shirin cin moriyar juna da nufin bunkasa kudaden shigar al'ummar masu karamin karfi sannan a hannu guda kuma domin biyan bukatun yau da kullum na magidanta mazauna birane, inji Wang.

Wang yace, gwamnatin tsakiya zata cigaba da sanya ido ga ayyukan samar da tallafi ga gundumomin kasar 52 masu fama da talauci, da bada fifiko wajen samar musu ruwan sha mai tsafta, da gidajen kwana, da ilmi, da aiwatar da shirin sauya matsagunai ga mazauna karkara.

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China