Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Kullum Sin na mai da hankali kan ingancin kayayyakin da ta fitar zuwa ketare
2020-04-02 19:48:05        cri
A yau a nan birnin Beijing, mai magana da yawun ma'aikatar harkokin wajen kasar Sin Hua Chunying ta bayyana cewa, kwanan baya wasu kafofin watsa labarai na Netherlands sun yi korafin cewa, abin rufe baki da hancin da ta saya daga kasar Sin ba shi da inganci, amma bayan binciken da hukumomin da abin ya shafa na kasar Sin suka yi, an nuna cewa, 'yan kasuwar ta Netherlands sun sayi wadannan abubuwan rufe baki da hanci daga kasar Sin, kuma kamfanin da ya samar da wadannan abubuwa na kasar Sin ya sanar da su cewa, wadannan abubuwan rufe baki da hancin ba na amfanin asibiti ba ne, kuma an bayyana haka, yayin da aka yi rajista a hukumar kwantam.

Madam Hua ta yi tsokacin ne saboda wasu kafofin watsa labarai na Netherlands da Belgium da sauran kasashen Turai sun wallafa rahotanni cewa, abubuwan rufe baki da hancin da suka shigo daga kasar Sin ba su da inganci.

Hua ta kara da cewa, abubuwan rufe baki da hanci suna da ma'aunin kandagarki iri daban daban, misali akwai na amfanin yau da kullum da kuma na amfani a asibiti, yanzu haka kasashen duniya suna bukatar kayayyakin kandagarkin annobar cutar numfashi ta COVID-19 matuka, shi ya sa ya dace a duba nau'in kayayyaki da yadda ake amfani da su kafin a saye su. Wasu kafofin watsa labarai sun koka kan ingancin kayayyakin kasar Sin kafin su gano hakikanin abubuwa, hakan bai dace ba, ana fatan ba sun yi hakan ne da mugun nufi ba, saboda hakan zai lalata hadin gwiwar dake tsakanin kasa da kasa yayin da suke dakile annobar tare.(Jamila)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China