Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Li Keqiang ya jagoranci taron magance COVID-19 da kwamitin tsakiyar JKS ya gabatar
2020-04-03 11:26:28        cri

Jiya Alhamis, firaministan kasar Sin, kana shugaban rukunin ba da jagoranci ga aikin yakar COVID-19 na kwamitin tsakiyar JKS ya jagoranci wani taro na rukunin.

Taron ya nuna cewa, kamata ya yi a kara karfin shawo kan mutanen da suke dauke da kwayar cutar COVID-19 marasa nuna alama, da daukar matakan tabbatar da rahoton aikin gwaji, da kebe kai, da na aikin jiyya, da kuma ba da kulawa ga wadanda suke da alaka da mutanen da suke dauke da kwayar cutar, har ma da gabatar da bayanai a kowace rana cikin lokaci.

Ban da wannan kuma, an kara karfin hana shigowar wadanda suka kamu da cutar daga ketare, saboda ganin yadda cutar ke saurin yaduwa a duniya.

Dadin dadawa, taron ya ce, kamata ya yi wurare daban-daban su daidaita matakan kandagarki kan yankuna, da kamfanoni, da kuma mutane na musamman bisa halin da suke ciki. Kaza lika a ingiza kokarin komawa bakin aiki, a wasu kamfanoni, da kantuna, da kuma kasuwanni, da laumbunan shan iska da dai sauransu, da wurare a yankunan da ba su da hadarin saurin yaduwar cutar, bisa matakan bude tawagogi, da kashe kwayoyi da kuma binciken lafiyar jikin ma'aikata.

Ban da wannan kuma, taron ya bayyana cewa, ya kamata a dauki matakin ingiza aikin kandagarkin cuta domin hana ta farfadowa, da bunkasuwar tattalin arziki na al'umma. Da kuma fitar da tsare-tsare masu inganci, don taimakawa kamfanoni, musamman ma wasu kanana, ta yadda za a sa kaimi ga farfado da masana'antu a dukkanin fannoni, da ba da tabbaci ga aikin samar da isassun kayayyaki, sannan kuma da kara karfin habaka bukatun cikin gida, ta hanyar raya sabbin masana'antu, da kyautata zaman rayuwar jama'a, da kuma ingiza karfin kamfanoni daban-daban a kasuwanni, da kara kafin farfadowar tattalin arziki. (Amina Xu)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China