![]() |
|
2020-04-02 20:28:02 cri |
Li wanda ya bayyana haka yayin taron manema labarai da hukumar ta shirya, ya ce, kasar Sin ta shafe kusan shekaru 57 tana tura tawagogin ma'aikatan lafiya zuwa kasashen nahiyar, yanzu haka akwai kimanin ma'aikatan lafiya 1,000 dake aiki a Afirka. Tun lokacin da cutar COVID-19 ta barke a nahiyar Afirka, hukumar lafiyar kasar Sin (NHC) ta umarci tawagogin lafiyarta dake Afirka, inda suka taimakawa kasashen da suke zaune, wajen yaki da wannan annoba da samar da horo da ma ilimantar da jama'a sau sama da 250, har mutane sama da 10,000 sun halarci shirin samun horon.
Ya ce, horon da tawagogin ma'aikatan lafiyar ta kasar Sin suka bayar a asibitocin kasashen na Afirka, sun kara kwarewar likitocin nahiyar ta gano, da ba da magani da jinyar marasa lafiya.
Haka kuma tawagogin ma'aikatan lafiyar kasar Sin, sun samar da bayanan yaki da cutar COVID-19 cikin harsuna da dama, matakin da ya haifar da kyakkyawan sakamako.(Ibrahim)
| ||||
® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China