Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Jami'in hukumar kula da miyagun kwayoyi na kasar Sin ya bukaci a tsaurara matakai kan magunguna masu cutarwa
2020-04-02 11:30:52        cri
Mamban majalisar gudanarwar kasar Sin Zhao Kezhi ya bukaci a kara azama wajen warware manyan matsalolin dake shafar aikin dakile ta'ammali da miyagun kwayoyi.

Zhao, wanda kuma shi ne daraktan kwamitin hana ta'ammali da miyagun kwayoyi na kasar Sin, yayi wannan tsokaci ne a taron yaki da fataucin kwayoyi na kasar da aka gudanar ta wayar tarho.

Da yake jaddada muhimmancin ayyukan yaki da ta'ammali da kwayoyi na wannan shekarar, Zhao ya bukaci a tsaurara matakan hana shigo da kwayoyi cikin kasar, da kyautata ayyukan kula da kwayoyi da daukar matakan dakile ayyukan samar da haramtattun kwayoyi.

Za'a kara bada fifiko a bangarorin dake da manyan matsaloli game da kwayoyi da yankunan dake fama da kangin talauci da suke da matsalolin ta'ammali da kwayoyi, inji Zhao.

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China