Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Al'ummar kasa da kasa suna son yin hadin gwiwa domin kare duniya
2020-04-02 15:38:53        cri
A halin yanzu, wato lokacin da ake fama da yaduwar cutar numfashi ta COVID-19 cikin kasa da kasa, kasar Sin wadda ta gano cutar da farko da kuma cimma nasarar dakile yaduwar cutar cikin gida, tana sa kaimi ga al'ummar kasar da su dawo bakin ayyukansu cikin himma da kwazo, yayin da take samar da taimako ga kasashen da suke da bukata. Ya zuwa ranar 31 ga wata, kasar Sin ta samar da taimakon gaggawa ga wasu kasashe da hukumar kiwon lafiyar duniya ta WHO, da kungiyar tarayyar kasashen Afika ta AU da kungiyar tarayyar kasashen kudu maso gabashin nahiyar Asiya ta ASEAN da dai sauransu da adadinsu ya kai 120. Ta kuma tura tawagogin kwararrun likitoci zuwa kasashe 7, yayin da ta gudanar da tarukan karawa juna sani kimanin 30 da kasashe da yankuna sama da dari daya ta kafar bidiyo, domin bayani kan fasahohinta na dakile yaduwar cutar numfashi ta COVID-19.

Amma wasu 'yan siyasa na yammacin kasashen duniya sun musanta kokarin da kasar Sin ta yi, har suke yunkurin bata mata suna.

Kuma dukkanin tsokacin da suka yi dake bata hadin gwiwar kasa da kasa ta fuskar yaki da annobar, sun zama abun zargi ga jama'ar kasa da kasa. A jiya Laraba, hukumar kiwon lafiya ta duniya WHO ta kira taron manema labarai game da cutar numfashi ta COVID-19 a birnin Geneva. A yayin taron, wakilin hukumar ya musanta zargin da kafofin watsa labaran waje ke yi wa kasar Sin cewa, wai ta boye alkalumanta game da cutar. Wakilin kula da harkokin gaggawa na hukumar WHO Mike Ryan ya bayyana cewa, cikin bayanan da kasashen duniya suka gabatarwa hukumar WHO cikin ko wace rana, akwai shaidu masu inganci da yawa da aka samu bisa kimiyya da fasaha. Kuma hukumar za ta yi hadin gwiwa da ko wace kasa domin samun sahihan bayanai. Ya ce, a sa'i daya kuma, ana ganin cewa, a wannan hali na musamma, abu ne mai wuya a sanar da dukkanin bayanai da alkaluman da aka samu cikin ko wane minti. Yanzu kuma, hukumar WHO ta samu bayanai game da yaduwar cutar numfashi ta COVID-19 daga kasashen Jamus, Singapore, Amurka da Sin, inda take godiya matuka dangane da bayanan da wadannan kasashen suka samar kan yaduwar annobar a matakin farko. Ya kuma kara da cewa, ana iya fahimtar cewa, sabo da wasu kasashe suna cikin yakin kare rayukan jama'a mai tsanani a halin yanzu, shi ya sa, ba su iya tattara bayanan da abin ya shafa yadda ya kamata ba.

Wani Masani a Nijeriya, ya yi sharhi a jaridar Vanguard ta kasar, inda ya yi kira ga shugabannin Amurka da su daina kiran cutar numfashi ta COVID-19 da "cutar Sin", da kuma hada gwiwa wajen yaki da cutar ta yadda za a iya kare bil adama yadda ya kamata.

Kamar yadda babban sakataren hukumar WHO Tedros Adhanom Ghebreyesus ya bayyana, cutar numfashi ta COVID-19 sabuwar cuta ce da aka gano, shi ya sa akwai abubuwa da yawa da ba a sani ba game da wannan cuta, kamar akwai wasu masu dauke da cutar da ba su nuna alamun kamuwa da cutar ba. Shi ya sa, ya kamata a fahimta tare da amincewa da kasa da kasa, yayin gudanar da bincike kan bayanan da hukumar ta samu yadda ya kamata. Kuma ana bukatar hadin gwiwar dukkanin al'ummomin kasa da kasa domin yaki da annobar, balle ma hadin gwiwar manyan kasashen biyu wato Amurka da Sin. (Maryam)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China