Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
WHO ta musanta zargin kafofin watsa labaran waje dake cewa Sin ta boye alkalumanta
2020-04-02 11:54:12        cri
Jiya Laraba, hukumar kiwon lafiya ta duniya WHO ta kira taron manema labarai game da cutar numfashi ta COVID-19 a birnin Geneva. A yayin taron, wakilin hukumar ya musanta zargin da kafofin watsa labaran waje ke yi wa kasar Sin cewa, wai ta boye alkalumanta game da cutar.

Wakilin kula da harkokin gaggawa na hukumar WHO Mike Ryan ya bayyana cewa, cikin bayanan da kasashen duniya suka gabatarwa hukumar WHO cikin ko wace rana, akwai shaidu masu inganci da yawa da aka samu bisa kimiyya da fasaha. Kuma hukumar za ta yi hadin gwiwa da ko wace kasa domin samun sahihan bayanai. Ya ce, a sa'i daya kuma, ana ganin cewa, a wannan hali na musamma, abu ne mai wuya sanar da dukkanin bayanai da alkaluman da aka samu cikin ko wane minti. Yanzu kuma, hukumar WHO ta samu bayanai game da yaduwar cutar numfashi ta COVID-19 daga kasashen Jamus, Singapore, Amurka da Sin, inda take godiya matuka dangane da bayanan da wadannan kasashen suka samar kan yaduwar annobar a matakin farko. Ya kuma kara da cewa, ana iya fahimtar cewa, sabo da wasu kasashe suna cikin yakin kare rayukan jama'a mai tsanani a halin yanzu, shi ya sa, ba su iya tattara bayanan da abin ya shafa yadda ya kamata ba.

Haka kuma, babban sakataren hukumar WHO Tedros Adhanom Ghebreyesus ya bayyana cewa, cutar numfashi ta COVID-19 sabuwar cuta ce da aka gano, akwai abubuwa da yawa da ba a sani ba game da wannan cuta, kamar akwai wasu masu dauke da cutar da ba su nuna alamun kamuwa da cutar ba. Shi ya sa, ya kamata a fahimta tare da amincewa da kasa da kasa, yayin gudanar da bincike kan bayanan da hukumar ta samu yadda ya kamata. (Maryam)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China