Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Kasar Sin tana adawa da bata sunanta da Amurka ta yi yayin da take kokarin dakile cutar COVID-19
2020-03-22 21:15:52        cri

A kwanakin nan ne, ba sau daya ba kuma ba sau biyu ba shugaban Amurka Donald Trump ya maye gurbin kalmar "coronavirus" da kalmomin "kwayar cutar China" masu nuna kabilanci a shafin sada zumunta da sauran wasu wurare. Kafofin watsa labaran Amurka sun nuna cewa, Trump na yunkurin dora laifin saurin yaduwar annobar a Amurka kan kasar Sin.

 

 

Amma bangarori daban-daban sun yi suka ga irin wannan aika-aikar bata sunan kasar Sin da Trump ya yi, ciki har da Hillary Clinton, inda a cewarta, Trump ya yi wannan furucin nuna kabilanci ne kawai domin karkatar da hankalin jama'a, domin wanke kansa daga laifuffukan da ya aikata, ciki har da jinkirin maida martani yadda ya kamata wajen dakile yaduwar kwayar cutar COVID-19, da rashin yin kyakkyawan shiri don shawo kan annobar a Amurka.

Hillary Clinton ta gayawa mutanen Amurka cewar, "kar ku yarda da maganar Trump, kar kuma abokai da iyalanku su yarda da shi."

 

 

Kasar Sin tana adawa da bata sunanta da Amurka ta yi yayin da take kokarin dakile cutar COVID-19. A ranar 18 da 19 ga wata, ministan harkokin wajen kasar Wang Yi ya zanta da takwarorinsa na kasashen Rasha, Netherlands, Singapore da kuma Faransa daya bayan daya, inda ya jadadda cewa, kasarsa na adawa da duk wani irin aikin bata suna. Ma'anar annoba bata san iyakar kasa ba, akwai bukatar kasashen duniya su hada kai don tinkararta. (Murtala Zhang)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China