Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
MDD ta sanar da matakan tunkarar COVID-19 a tsakanin 'yan gudun hijirar dake arewa maso gabashin Nijeriya
2020-04-01 12:16:34        cri
MDD ta ce tana shirin gaggawa tare da daukar matakan dakile yaduwar annobar COVID -19 a tsakanin mutane mafi rauni da rikici ya rutsa da su a arewa maso gabashin Nijeriya.

Wata sanarwa da ta shiga hannun kamfanin dillancin labarai na Xinhua jiya a Lagos, ta ruwaito Edward Kallon, shugaban shirin agajin jin kai na MDD a Nijeriya na cewa, matakan za kuma su shawo kan bukatun gaggawa da annobar ka iya haifarwa.

Ya ce ba za su jira annobar ta isa sansanonin 'yan gudun hijira kafin su dau mataki ba. Ya ce 'yan gudun hijirar sun shiga mawuyacin hali sabili da rikicin da ya shafe shekaru 10 ana yi, inda ya ce abun da za su mayar da hankali a kai shi ne, tabbatar da an ci gaba da kai musu dauki, musammam na kiwon lafiya, ga mata da yara da tsoffin mafi rauni, wadanda ke bukatar kulawa ta musammam.

A cewarsa, ofishin MDD dake Nijeriya, na taimakawa gwamnatocin jihohin Borno da Adamawa da Yobe, wajen samar da dabarun tunkarar cutar, wadanda ke la'akari da halin da ake ciki a yankuna da sansanonin 'yan gudun hijira. (Fa'izaMustapha)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China