Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Kasar Sin ta zuba kusan yuan biliyan 25 a bangaren tallafin kiwon lafiya
2020-04-02 11:25:11        cri

Kasar ta ware yuan biliyan 24.5, kwatankwacin dala biliyan 3.45 ga bangaren tallafin kiwon lafiya a shekarar 2019, ciki har da biliyan 4 da aka ware wajen inganta harkar inshorar lafiya a yankunan dake fama da matsanancin talauci.

Hukumar kula da inshorar lafiya ta kasar, ta ce a 2019, sama da mutane miliyan 77 da suka ci gajiyar tallafin, sun rattaba hannu kan tsarin inshorar lafiya a matakin farko.

Kasar Sin ta gina tsarin inshorar lafiya a matakin farko da na inshorar manyan cututtuka da tallafin magunguna domin yaki da talauci ta hanyar kiwon lafiya.

Zuwa karshen 2019, mutane miliyan 200 ne suka ci gajiyar irin wadancan shirye-shirye, kuma mutane miliyan 4.18 da suka fada cikin talauci saboda rashin lafiya, sun fito daga kangin.

Har ila yau, zuwa karshen baran, tsarin inshorar lafiya a matakin farko ya mamamye sama da kaso 99.9 na al'ummun dake fama da talauci a yankunan karkara na kasar. (Fa'iza Mustaphha)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China