Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Akwai sabbin mutane 15 da aka tabbatar sun kamu da cutar COVID-19 a babban yankin kasar Sin a jiya Laraba
2020-03-12 11:48:18        cri

Hukumar lafiyar kasar Sin ta fidda labari cewa, an gano sabbin mutane 15 da suka kamu da cutar numfashi ta COVID-19 a babban yankin kasar Sin, da kuma mutane 11 da cutar ta hallaka jiya Laraba. Sa'an nan, an sallami mutane 1,318 daga asibiti bayan sun warke daga cutar.

Ya zuwa jiya Laraba, gaba daya wadanda aka tabbatar sun kamu da cutar a babban yankin kasar Sin ya kai 80,793, yayin da aka sallami mutane 62,793 bayan sun warke daga cutar, sai kuma mutane 3,169 da cutar ta hallaka.

Bugu da kari, bisa labarin da hukumar lafiyar lardin Hubei ta fidda, an ce, a jiya Laraba, akwai sabbin mutane 8 da aka tabbatar sun kamu da cutar a lardin, kuma dukkansu daga birnin Wuhan suke, wannan shi ne karo na farko da adadin ya sauka zuwa kasa da 10. (Maryam)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China