Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Yawan abin rufe baki da hanci masu amfani da likitanci na N95 da Sin ta samar a kowace rana ya kai miliyan daya
2020-02-27 12:07:42        cri

Hukumar raya kasa da yin kwaskwarima ta kasar Sin ta sanar a jiya cewa, ya zuwa ranar 24 ga wannan wata, yawan abin rufe baki da hanci masu amfani da likitanci na N95 da Sin ta samar a kowace rana ya kai miliyan daya da dubu 70, wanda ya karu da yawansu na ranar 1 ga wannan wata ninka sau 4.7.

A kwanakin baya, hukumar raya kasa da yin kwaskwarima ta kasar Sin ta dauki matakai masu amfani don sa kaimi ga mayar da ayyukan kamfanoni da samar da kayayyaki, da nuna goyon baya ga kara samar da kayayyaki, da daidaita aikin samar da muhimman kayayyaki da na'urori don tabbatar da samar da abin rufe baki da hanci yadda ya kamata.

An gudanar da aikin daidaita kayayyakin da aka samar ga dukkan kasar Sin, da tabbatar da samar da kayayyaki ga muhimman yankuna kamar lardin Hubei. Tun daga ranar 1 zuwa 25 ga wannan wata, yawan abin rufe baki da hanci masu amfani da likitanci na N95 da aka tura zuwa lardin Hubei ya kai miliyan 3 da dubu 40. An tura wurin da abin ya shafa dubu 150 a kowace rana a wadannan kwanaki, kana an kiyaye samar dasu a cikin lardin Hubei, yanzu ana iya biyan bukatun likitoci da suke yin aikin yaki da cutar numfashi ta COVID-19 a wurin. (Zainab)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China