Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Wang Yi: Sin na son hada kai da Japan da Koriya ta Kudu wajen yaki da cutar COVID-19
2020-02-27 12:25:03        cri

Jiya Laraba, mamban majalisar gudanawar kasar Sin, kana ministan harkokin wajen kasar Wang Yi ya yi shawarwari ta wayar tarho da takwaransa na kasar Japan Motegi Toshimitsu, inda ya ce, kasar Sin tana farin ciki sosai bisa goyon bayan da kasar Japan ta nuna mata, haka kuma tana godiya matuka dangane da taimako da goyon baya da gwamnati da al'ummomin kasar Japan suka baiwa kasar Sin. Game da batun yaki da cutar numfashi ta COVID-19, Sin da kasar Japan tamkar 'yan uwa ne, ya kamata kasashen biyu su karfafa mu'amalar dake tsakaninsu, domin fuskantar cutar yadda ya kamata, da ma hana yaduwar ta a sauran sassa na duniya, ta yadda za a iya kiyaye tsaron kiwon lafiyar jama'ar kasa da na yankin baki daya.

A nasa bangare, Motegi Toshimitsu ya yi bayani kan yanayin cutar numfashi ta COVID-19 a kasar Japan, ya ce, gwamnatin kasar Japan ta tsara dabarun fuskantar hana yaduwar cutar a kasar baki daya. Ya kuma nuna fatan kara yin mu'amala da kasar Sin kan harkokin da suka shafi cutar numfashi ta COVID-19.

Bugu da kari, Wang Yi ya yi shawarwari da takwaransa ta kasar Koriya ta Kudu Kyung-wha Kang ta wayar tarho, inda ya ce, matsalar kasar Koriya ta Kudu matsalar kasar Sin ce, kasar Sin tana son ba da dukkanin taimakon da kasar Koriya ta Kudu take bukata, domin taimakawa gwamnati da al'ummomin kasar Koriya ta Kudu wajen yaki da cutar numfashi ta COVID-19.

A nata jawabin, Kyung-wha Kang ta yi bayani kan matakan da kasar Koriya ta Kudu ta dauka domin fuskantar cutar numfashi ta COVID-19, ta ce, kasarta za ta iya hana yaduwar cutar numfashi ta COVID-19 a cikin kasar, kuma tana fatan kara hadin gwiwa da mu'amala da kasar Sin domin fuskantar wannan matsala. (Maryam)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China