Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Sojojin Sin suna cikin yaki da cutar numfashi ta COVID-19
2020-02-27 15:19:50        cri

Mu kan kira rundunar sojan kasar Sin "sojoji na yaran al'ummar kasa", ma'anar ita ce asalinsu shi ne al'ummar kasa, suna kuma bautawa al'ummar kasa. A duk lokacin da aka gamu da babbar matsala, rundunar sojan kasar Sin ta kan fito nan take ta tinkari matsalar. Kafin zuwan bikin bazara, wato sabuwar shekarar kasar Sin bisa kalandar gargajiya, cutar numfashi ta COVID-19 ta bullo a kasar, kuma saboda barkewar wannan annobar, sojojin kasar Sin sun fara aikinsu.

A ranar 24 ga watan Janairu, wato rana ta biyu da aka rufe birnin Wuhan na kasar Sin, rundunar sojan kasar Sin ta aike da tawagogin ma'aikatan lafiya guda uku, wadanda suka hada da mutane 450 zuwa birnin Wuhan. Sa'an nan, a ranar 2 ga wata, da ranar 13 ga wata, da ranar 17 ga wata, rundunar sojan kasar Sin ta yi amfani da jiragen saman sufuri guda 27 domin tura ma'aikatan lafiya na rundunar soja sama da 2400 da kayayyaki sama da ton dari daya zuwa birnin Wuhan.

A halin yanzu, rundunar sojan kasar Sin ta riga ta tura ma'aikatan lafiya sama da dubu 4 zuwa birnin Wuhan, inda suka yi hadin gwiwa da sauran ma'aikatan lafiya kimanin dubu 30 wadanda suka zo daga wurare daban daban na kasar Sin domin ba da jinya ga wadanda suka kamu da cutar numfashi ta COVID-19 a asibitocin dake samun yawancin masu kamuwa da cutar da asibitocin wucin gadi. Kana, wasu daga cikin wadannan ma'aikatan lafiya na rundunar soja sun taba halartar yaki na cutar SARS a shekarar 2003, wasu kuma sun taba ba da taimako ga kasashen Saliyo da Liberia wajen yaki da cutar Ebola.

Cikin wannan yaki da cutar numfashi ta COVID-19, sojojin kasar Sin sun nuna kyakkyawar halayyarsu na nuna jaruntaka da kwarewarsu kan ayyukan, haka kuma, rundunar sojan kasar tana ci gaba da kyautata kwarewarta ta fuskar ayyuka daban daban bisa sabbin na'urorin soja da aka samar, kamar babban jirgin saman sufuri na Y-20 da sauransu.

Da samun rundunar soja mai karfi kamar haka a matsayin babban goyon baya na al'ummar Sin, tabbas ne kasar Sin za ta cimma nasarar wannan yaki na cutar numfashi ta COVID-19. (Maryam)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China